MUSABAKA A MAHANGAR MUSULUNCI (IBRAHIM JALO JALINGO)
Da yawa daga cikin wadanda suka
zaba wa kansu sabanin shiriyar
Manzon Allah cikin gudanar da
addininsu suna ganin cewa: In har
Idin Maulidi bidi’ah ne, to kuwa lalle
Musabaka a kan haddar Alqur’ani Mai
girma, ko haddar Hadithan Annabi
masu daraja ko haddar wani ilmi na
Musulunci su ma yin su bidi’ah ce!!!
*************************
A nan muna ganin cewa yawan
nisantar wadannan mutane ga
littattafan Shari’ah na maluman
Musulunci ne ya sa ba su ma san
cewa: Dukkan abin da halaccinsa ya
tabbata ta yanyar Ijma’in Musulmi
cikin wani zamani daga cikin zamuna,
to dole ne ya zamanto daya daga cikin
abubuwa uku:-
1- ko dai ya zamanto Mubaahi, watau
abin da yin sa da rashin yin sa duk
daya a idanun Shari’ah.
2- ko kuwa ya zamanto Mustahabbi,
watau abin da in har ba a yi shi ba to
ba a yi wani laifi ba, in kuma aka yi
shi to ana da wani lada na
musamman.
3- ko kuwa ya zamanto Waajibi, watau
abin da in har ba a yi shi ba za a sami
zunubi, in kuma an yi shi to an yi
abin da Shari’ah ta tilasta yin shi.
******************************
shi kuwa Musabaka domin haddar
Alqur’ani Mai girma abu ne da
Maluman Sunnah, da su kansu masu
bidi’ah na Duniya suka hadu a kan
halaccinsa a bisa hujjar kiyasin shi a
kan Musaabakokin da Nassi ya zo da
halaccinsu. In kuwa haka lamarin
yake, to ta kaka ne za a hada hukuncin
Musaabaka domin haddar Alqur’ani
da hukuncin Idin Maulidin da babu
mai yin shi ko halatta shi in banda
wasu daga cikin masu yin bidi’ah??
*********************
HUKUNCIN MUSABAKA:
1. Imam Ibnu Qudaamah mai rasuwa
a shekara ta 620 watau da mutuwarsa
yau shekaru 815 ke nan, ya ce cikin
littafinsa mai suna Almugnii
13/404-405 :-
{ ﻟﻤﺴﺎﺑﻘﺔ ﺟﺎﺋﺰﺓ ﺑﺎﻟﺴﻨﺔ ﻭﺍﻻﺟﻤﺎﻉ، ﺍﻣﺎ ﺍﻟﺴﻨﺔ
ﻓﺮﻭﻯ ﺍﺑﻦ ﻋﻤﺮ ﺍﻥ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ
ﺳﺎﺑﻖ ﺑﻴﻦ ﺍﻟﺨﻴﻞ ﺍﻟﻤﻀﻤﺮﺓ ﻣﻦ ﺍﻟﺤﻔﻴﺎﺀ ﺍﻟﻰ
ﺛﻨﻴﺔ ﺍﻟﻮﺩﺍﻉ، ﻭﺑﻴﻦ ﺍﻟﺘﻲ ﻟﻢ ﺗﻀﻤﺮ ﻣﻦ ﺛﻨﻴﺔ
ﺍﻟﻮﺩﺍﻉ ﺍﻟﻰ ﻣﺴﺠﺪ ﺑﻨﻲ ﺯﺭﻳﻖ. ﻣﺘﻔﻖ ﻋﻠﻴﻪ…
ﻭﺍﺟﻤﻊ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻮﻥ ﻋﻠﻰ ﺟﻮﺍﺯ ﺍﻟﻤﺴﺎﺑﻘﺔ ﻓﻲ
ﺍﻟﺠﻤﻠﺔ. ﻭﺍﻟﻤﺴﺎﺑﻘﺔ ﻋﻠﻰ ﺿﺮﺑﻴﻦ : ﻣﺴﺎﺑﻘﺔ ﺑﻐﻴﺮ
ﻋﻮﺽ، ﻭﻣﺴﺎﺑﻘﺔ ﺑﻌﻮﺽ. ﻓﺎﻟﻤﺴﺎﺑﻘﺔ ﺑﻐﻴﺮ ﻋﻮﺽ
ﻓﺘﺠﻮﺯ ﻣﻄﻠﻘﺎ ﻣﻦ ﻏﻴﺮ ﺗﻘﻴﻴﺪ ﺑﺸﻲﺀ ﻣﻌﻴﻦ،
ﻛﺎﻟﻤﺴﺎﺑﻘﺔ ﻋﻠﻰ ﺍﻻﻗﺪﺍﻡ، ﻭﺍﻟﺴﻔﻦ، ﻭﺍﻟﻄﻴﻮﺭ،
ﻭﺍﻟﺒﻐﺎﻝ، ﻭﺍﻟﺤﻤﺮ، ﻭﺍﻟﻤﺰﺍﺭﻳﻖ، ﻭﺍﻟﻤﺼﺎﺭﻋﺔ، ﻭﺭﻓﻊ
ﺍﻟﺤﺠﺮ ﻟﻴﻌﺮﻑ ﺍﻻﺷﺪ، ﻭﻏﻴﺮ ﺫﻟﻚ؛ ﻻﻥ ﺍﻟﻨﺒﻲ
ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻛﺎﻥ ﻓﻲ ﺳﻔﺮ ﻣﻊ ﻋﺎﺋﺸﺔ
ﻓﺴﺎﺑﻘﺘﻪ ﻋﻠﻰ ﺭﺟﻠﻬﺎ، ﻓﺴﺒﻘﺘﻪ، ﻗﺎﻟﺖ : ﻓﻠﻤﺎ
ﺣﻤﻠﺖ ﺍﻟﻠﺤﻢ ﺳﺎﺑﻘﺘﻪ ﻓﺴﺒﻘﻨﻲ، ﻓﻘﺎﻝ : ﻫﺬﻩ
ﺑﺘﻠﻚ. ﺭﻭﺍﻩ ﺍﺑﻮﺩﺍﻭﺩ. ﻭﺳﺎﺑﻖ ﺳﻠﻤﺔ ﺑﻦ ﺍﻻﻛﻮﻉ
ﺭﺟﻼ ﻣﻦ ﺍﻻﻧﺼﺎﺭ ﺑﻴﻦ ﻳﺪﻱ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ
ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻓﻲ ﻳﻮﻡ ﺫﻱ ﻗﺮﺩ. ﻭﺻﺎﺭﻉ ﺍﻟﻨﺒﻲ
ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺭﻛﺎﻧﺔ ﻓﺼﺮﻋﻪ. ﺭﻭﺍﻩ
ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ. ﻭﻣﺮ ﺑﻘﻮﻡ ﻳﺮﺑﻌﻮﻥ ﺣﺠﺮﺍ ﻳﻌﻨﻲ
ﻳﺮﻓﻌﻮﻧﻪ ﻟﻴﻌﺮﻓﻮﺍ ﺍﻻﺷﺪ ﻣﻨﻬﻢ ﻓﻠﻢ ﻳﻨﻜﺮ ﻋﻠﻴﻬﻢ.
ﻭﺳﺎﺋﺮ ﺍﻟﻤﺴﺎﺑﻘﺎﺕ ﻳﻘﺎﺱ ﻋﻠﻰ ﻫﺬﺍ .{ ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Musabaka halal ce cikin
sunnar Manzon Allah, da Ijma’in
Maluma. A cikin Sunnah dai Ibnu
Umar ya ruwaito cewa Annabi mai
tsira da amincin Allah ya shirya
Musabaka tsakanin dawakin da aka yi
musu “Tadhmiir” (watau wadanda aka
yi musu horon tinkarar yaki ta hanyar
karanta abinci gare su da sanya musu
tufafinsu da sauransu) a filin da ya
taso daga Haifaa har zuwa
Thaniyyatul Wadaa, haka nan ya
shirya wata Musabakar tsakanin
dawakin da ba a yi musu Tadhmiiri
ba, a filin da ya taso daga Thaniyyatul
Wadaa har zuwa Masjidu Bani Zuraiq.
Buhari da Muslim ne suka ruwaito
hadithin…Sannan Musulmi sun yi
Ijma’i a kan halaccin Musabaka a
dunkule. Sannan ita Musabaka ta kasu
ne zuwa kashi biyu: Musabaka da ake
yi tare da sanya wasu kudi cikinta (ga
duk wanda ya yi nasara). Akwai kuma
Musabaka da ake yi ba tare da an
sanya kudi cikinta (ga duk wanda ya
yi nasara ba). To ita Musabaka da ake
yi ba tare da an sanya wasu kudi
cikinta ba wannan ta halatta ba tare
da sanya mata wani tarnaki a cikinta
ba, kamar dai Musabakar da ake yi na
tseren gudu da kafa, ko Musabakar
tseren jiragen ruwa, ko Musabakar
tsere tsakanin tsutsaye, ko Musabakar
tsere tsakanin alfadaru, ko Musabakar
tsere tsakanin jakuna, ko Musabakar
tsere tsakanin giwaye, ko Musabakar
yin harbi da kananan masu, ko
Musabakar yin kokowa, ko Musabakar
daga dutse mai nauyi sanoda gwada
karfi, da dai nau’o’in Musabaka
dabam daban. Saboda Annbi mai tsira
da amincin Allah wata rana a hanyar
tafiye-tafiyensa ya yi Musabakar
tseren gudu da kafa tsakaninsa da
matarsa Nana A’isha Allah Ya kara
mata yarda, kuma ta yi nasara a
kansa. Sai A’isha ta ce: da na yi kiba
sai wata rana muka sake yin
Musabakar tseren gudu da kafa sai ya
yi nasara a kaina. Sai ya ce da ni: ni
ma na rama wancan ci da kika yi
mini. Wannan hadithi Abu Dawuda ne
ya ruwaito shi. Kuma Salamah Dan
Ak’wa ya yi Musabakar tsere da kafa
tsakaninsa da wani mutum a gaban
Annabi mai tsira da amincin Allah a
ranar Ruwan Zuu Qarad. Sannan
Annabi mai tsira da amincin Allah ya
yi Musabakar kokowa tsakaninsa da
wani gwanin kokowa mai suna
Rukaanah, kuma ya yi nasara a kansa
ya kada shi. Tirmizii ne ya ruwaito
hafithin. Sannan wata rana Annabi
mai tsira da amincin Allah ya wuce
wasu mutane suna Musabakar daga
dutse mai nauyi saboda sanin wane ne
ya fi karfi, amma bai hana su yin
hakan ba. Sauran Musabakpkin sai a
kiyasta su a kan wadannan)) [da nassi
ya tabbatar]. Intaha.
2. Imamu Ibnu Qayyimil Jauziyyah
wanda ya mutu a shekarar Hijira ta
751 watau yau shekaru 684 ke nan da
suka wuce ya ce cikin littafinsa mai
suna Alfuruusiyyah 1/318:-
{ ﺍﻟﻤﺴﺎﻟﺔ ﺍﻟﺤﺎﺩﻳﺔ ﻋﺸﺮﺓ : ﺍﻟﻤﺴﺎﺑﻘﺔ ﻋﻠﻰ ﺣﻔﻆ
ﺍﻟﻘﺮﺍﻥ، ﻭﺍﻟﺤﺪﻳﺚ، ﻭﺍﻟﻔﻘﻪ، ﻭﻏﻴﺮﻩ ﻣﻦ ﺍﻟﻌﻠﻮﻡ
ﺍﻟﻨﺎﻓﻌﺔ، ﻭﺍﻻﺻﺎﺑﺔ ﻓﻲ ﺍﻟﻤﺴﺎﺋﻞ، ﻫﻞ ﺗﺠﻮﺯ
ﺑﻌﻮﺽ؟ ﻣﻨﻌﻪ ﺍﺻﺤﺎﺏ ﻣﺎﻟﻚ، ﻭﺍﺣﻤﺪ،
ﻭﺍﻟﺸﺎﻓﻌﻲ . ﻭﺟﻮﺯﻩ ﺍﺻﺤﺎﺏ ﺍﺑﻲ ﺣﻨﻴﻔﺔ،
ﻭﺷﻴﺨﻨﺎ، ﻭﺣﻜﺎﻩ ﺍﺑﻦ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﺒﺮ ﻋﻦ ﺍﻟﺸﺎﻓﻌﻲ.
ﻭﻫﻮ ﺍﻭﻟﻰ ﻣﻦ ﺍﻟﺸﺒﺎﻙ، ﻭﺍﻟﺼﺮﺍﻉ، ﻭﺍﻟﺴﺒﺎﺣﺔ،
ﻓﻤﻦ ﺟﻮﺯ ﺍﻟﻤﺴﺎﺑﻘﺔ ﻋﻠﻴﻬﺎ ﺑﻌﻮﺽ، ﻓﺎﻟﻤﺴﺎﺑﻘﺔ
ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻌﻠﻢ ﺍﻭﻟﻰ ﺑﺎﻟﺠﻮﺍﺯ، ﻭﻫﻲ ﺻﻮﺭﺓ ﻣﺮﺍﻫﻨﺔ
ﺍﻟﺼﺪﻳﻖ ﻟﻜﻔﺎﺭ ﻗﺮﻳﺶ ﻋﻠﻰ ﺻﺤﺔ ﻣﺎ ﺍﺧﺒﺮﻫﻢ
ﺑﻪ، ﻭﺛﺒﻮﺗﻪ. ﻭﻗﺪ ﺗﻘﺪﻡ ﺍﻧﻪ ﻟﻢ ﻳﻘﻢ ﺩﻟﻴﻞ ﺷﺮﻋﻲ
ﻋﻠﻰ ﻧﺴﺨﻪ . ﻭﺍﻥ ﺍﻟﺼﺪﻳﻖ ﺍﺧﺬ ﺭﻫﻨﻬﻢ ﺑﻌﺪ
ﺗﺤﺮﻳﻢ ﺍﻟﻘﻤﺎﺭ. ﻭﺍﻥ ﺍﻟﺪﻳﻦ ﻗﻴﺎﻣﻪ ﺑﺎﻟﺤﺠﺔ،
ﻭﺍﻟﺠﻬﺎﺩ، ﻓﺎﺫﺍ ﺟﺎﺯﺕ ﺍﻟﻤﺮﺍﻫﻨﺔ ﻋﻠﻰ ﺍﻻﺕ
ﺍﻟﺠﻬﺎﺩ، ﻓﻬﻲ ﻓﻲ ﺍﻟﻌﻠﻢ ﺍﻭﻟﻰ ﺑﺎﻟﺠﻮﺍﺯ. ﻭﻫﺬﺍ
ﺍﻟﻘﻮﻝ ﻫﻮ ﺍﻟﺮﺍﺟﺢ .{ ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Mas’alah ta goma sha daya:
Yin Musabakar haddace Alkur’ani, da
Hadithi, da Fiqhu, da wasu
Ilmummuka masu amfani, ko gane
abin da yake daidai cikin wasu
mas’alolin, shirya irin wannan
Musabaka a bisa wani kudi, shin
hakan zai halatta ko kuwa ba zai
halatta ba? Mutanen Malik, da Ahmad,
da Sha’fi’ii sun hana yin sa. Amma
mutanen Abu Hanifah da Malaminmu
(Ibnu Taimiyah) da ma hikayar Ibnu
Abdil Barr daga Sha’fi’ii sun halatta
yinsa. Shi wannan nau’i na Musabaka
ya fi yin Musabaka a kan harkar iya
sa tarko, ko kokowa, ko ninkaya,
sanoda haka wadanda suka halatta
shirya Musabaka a bisa kudi cikin
wadannan, lalle shirya Musabaka
cikin harkokin habaka ilmi shi zai fi
cancantar halatta, kuma wannan ita
ce surar Muraahanar da Sbubakar
Siddiq ya yi da kafuran Quraishawa a
kan gaskiyar labarin da ya ba su (na
cewa Ruumaawa za su yi nasara a kan
Faatisaawa bayan shekaru kadan).
Dalili ya gabata na cewa babu abin da
ya shafe ingancin wannan
Muraahanar. Kuma shi Abubakar ya yi
Muraahanar da su ne bayan haramta
yin caca. Sannan ita tsayuwar Addini
da ma tana samuwa ne ta hanyar kafa
hujja, da yin jihadi, saboda wannan
idan har Muraahanah za ta halatta a
kan abubuwan karfafa jihadi, ke nan
ta halatta a kan abubuwan karfafa
ilmi da za su karfafa kafa hujja shi ne
zai fi cancanta, kuma wannan magana
ita ce abin rinjayarwa)). Intaha.
******************************
Lalle da wadannan bayanai ne
mahankalta za su fahimci cewa ita
Musabakar haddar Alkur’ani mai
girma, ko musabakar haddar Hadithan
Manzon Allah Masu daraja, ko
musabakar haddar wani ilmi mai
amfani -tare da sanya wani kudi ga
wanda ya yi nasara ko kuwa ba tare
da sanya wani kudi ga wanda ya yi
nasara ba- abu ne da yake halal ta
hanyar hujjoji biyu:-
1. Ijma’i.
2. Qiyaasi.
Wannan kuwa duka sabanin maida
ranar haihuwar Annabi mai tsira da
amincin Allah wani Idi ne, wanda
babu Ijma’i a kansa, babu kuma wani
Qiyaasi sahihi a kansa. Muna rokon
Allah Ya taimake mu Ya tabbatar da
dugaduganmu a kan Sunnar Annabi
mai tsira da amincin Allah. Ameen.
Created at 2015-11-28 07:56
Back to posts
UNDER MAINTENANCE