HomeBlogAbout me

HUJJAR AHLUS SUNNAH A KAN RASHIN YIN KUNUTIN DIN-DIN- DIN NA SALLAR ASUBA (Dr.Ibrahim Jalo Jalingo)

HUJJAR AHLUS SUNNAH A KAN RASHIN YIN KUNUTIN DIN-DIN- DIN NA SALLAR ASUBA (Dr.Ibrahim Jalo Jalingo)
‘Yan’uwa Musulmi masu daraja! Lalle Ahlus Sunnan da ba sa karanta Kunutin din-din-din na Sallar Asuba suna yin hakan ne saboda riko da Sahihiyar Sunnah ba wai saboda son zuciya ko neman kare girman wani jagoran wata bidi’ah ba. A wannan dan takaitaccen bayani zan ambaci Hadithai biyu ne kacal masu ingancin isnadi, muna kuma fata Al’umma za su gamsu:- 1- Imam Ibnu Khuzaimah ya ruwaito hadithi na 619, cikin Sahihinsa, da kuma Imamut Tabarii hadithi na 2598 cikin Tahziibul A’athar, daga Sahabi Abu Hurairah Allah Ya kara masa yarda ya ce:- (( ﺍﻥ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻛﺎﻥ ﻻ ﻳﻘﻨﺖ ﺍﻻ ﺍﻥ ﻳﺪﻋﻮ ﻻﺣﺪ ﺍﻭ ﻳﺪﻋﻮ ﻋﻠﻰ ﺍﺣﺪ )). Ma’ana: ((Lalle Annabi mai tsira da amincin Allah ya kasance ba ya yin Kunuti sai dai in zai yi wa wani addu’ar alheri, ko kuwa zai yi wa wani mugunyar aduu’a)). Wannan Hadithi Shaikul Al’azumii ya inganta shi. 2- Imamut Tirmizii ya ruwaito hadithi na 402 cikin Sunan, daga Abu Maalik Al’ashja’ii ya ce:- (( ﻗﻠﺖ ﻻﺑﻲ ﻳﺎ ﺍﺑﺔ! ﺍﻧﻚ ﻗﺪ ﺻﻠﻴﺖ ﺧﻠﻒ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻭﺍﺑﻲ ﺑﻜﺮ ﻭﻋﻤﺮ ﻭﻋﺜﻤﺎﻥ ﻭﻋﻠﻲ ﺑﻦ ﺍﺑﻲ ﻃﺎﻟﺐ ﻫﻬﻨﺎ ﺑﺎﻟﻜﻮﻓﺔ ﻧﺤﻮﺍ ﻣﻦ ﺧﻤﺴﻴﻦ ﺳﻨﺔ، ﺍﻛﺎﻧﻮﺍ ﻳﻘﻨﺘﻮﻥ؟ ﻗﺎﻝ : ﺍﻱ ﺑﻨﻲ ! ﻣﺤﺪﺙ)). Ma’ana: ((Na ce wa babana: Ya Baba! Lalle kai ka yi salla bayan Manzon Allah mai tsira da amincin Allah, da Abu Bakar, da Umar, da Uthman, da Aliyyu Dan Abii Taalib a nan Kufah kusan shekara hamsin, ko sun kasance suna yin Kunuti? Sai ya ce: Ya kai Dana, ai bidi’ah ce)). Wannan Hadithi Albaanii ya inganta shi. ************************* Sannan Shaikhul Islam Ibnu Taimiyah ya ce cikin littafinsa Majmuu’ul Fataawa 22/372:- (( ﻭﺍﻟﺬﻱ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻫﻞ ﺍﻟﻤﻌﺮﻓﺔ ﺑﺎﻟﺤﺪﻳﺚ ﺍﻧﻪ ﻗﻨﺖ ﻟﺴﺒﺐ ﻭﺗﺮﻛﻪ ﻟﺰﻭﺍﻝ ﺍﻟﺴﺒﺐ )). Ma’ana: ((Abin da dai Masana ilmin Hadithi ke kansa shi ne: (Shi dai Annabi) ya yi Kunuti ne saboda wani dalili, kuma ya bar yin Kunutin saboda gushewar dalilin)). ******************* To amma idan wani ya ce: Ai Imam Ahmad ya ruwaito hadithi na 12679 cikin Musnad daga Sahabi Anas Dan Maalik cewa:- (( ﻣﺎ ﺯﺍﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻳﻘﻨﺖ ﻓﻲ ﺍﻟﻔﺠﺮ ﺣﺘﻰ ﻓﺎﺭﻕ ﺍﻟﺪﻧﻴﺎ )). Ma’ana: ((Manzon Allah mai tsira da amincin Allah bai gushe ba yana yin Kunuti cikin Sallar Asuba har ya bar Duniya)). Sai mu ce da shi: wannan Hadithi ba zai cancanci a kafa hujja da shi ba, saboda hidithi ne mai rauni. Imamul Albaanii ya ce cikin Silsilah Sahihah a karkashin lambar Hadithi na 5574: Hadithi ne munkari ba ya inganta. Haka nan shi ma Sheik Shu’aibul Arnaa’ut ya ce hadithi ne dha’iifi.
Back to posts
This post has no comments - be the first one!

UNDER MAINTENANCE

Snack's 1967