HomeBlogAbout me

BANBANCIN FAHIMTAN MALLAMAI AKAN BUDE TARO KO RUFE TA (IBRAHIM JALO JALINGO)

A wannan darasi namu za mu magana ne a kan kuskuren fahimtar nassin Alkur'ani Mai girma, ko nassin hadithan manzon Allah mai tsira da amincin Allah da wasu mutane ke yi game da bayanan da Malaman Sunnah ke yi na hukuncin maida bude taro ko rufe shi da addu'ah a cikin jam'i wata sunnar da ake maimaitawa a kullum. Ina rokon Allah da Ya buda zukatan 'yan'uwa domin su fahimci gaskiya su karbe ta. Ameen. *********************************** 'Yan'uwa Musulmi! Abin da malaman Sunnah ke cewa shi ne: A daina rikon bude taro ko rufe shi da addu'a a matsayin wata Sunnar da ake maimaitawa a kullum, ta yadda imma ba a yi addu'ar ba sai a rika ganin an bar wata falala mai yawa ta wuce, alhalin shi wannan lamari na bude taro da addu'a babu inda aka ga cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya yi shi koda sau daya ne duk kuwa da cewa yana da damar yin hakan da yin hakan wani alheri ne, ke nan malaman Sunnah sun fahimta daga hakan cewa: Sunnar Annabi mai tsira da amincin Allah cikin mas'alar ita ce rashin aikata hakan, domin kamar yadda daliban ilmi ne suka san cewa: wani lokaci Sunnah ta kan kasance ne ta hanyar bari, wani lokacin kuwa ta kan kasance ne ta hanyar yi. *********************************************** Babban Malami a duniyar Sunnah Shaikhul Islam Ibnu Taimiyah-Allah Ya yi masa rahama- ya ce cikin littafinsa Majmuu'ul Fataawa 26/172 :- (( ﻭﺍﻟﺘﺮﻙ ﺍﻟﺮﺍﺗﺐ ﺳﻨﺔ، ﻛﻤﺎ ﺍﻥ ﺍﻟﻔﻌﻞ ﺍﻟﺮﺍﺗﺐ ﺳﻨﺔ، ﺑﺨﻼﻑ ﻣﺎ ﻛﺎﻥ ﺗﺮﻛﻪ ﻟﻌﺪﻡ ﻣﻘﺘﺾ، ﺍﻭ ﻓﻮﺍﺕ ﺷﺮﻁ، ﺍﻭ ﻭﺟﻮﺩ ﻣﺎﻧﻊ، ﻭﺣﺪﺙ ﺑﻌﺪﻩ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﻘﺘﻀﻴﺎﺕ ﻭﺍﻟﺸﺮﻭﻁ ﻭﺯﻭﺍﻝ ﺍﻟﻤﺎﻧﻊ ﻣﺎ ﺩﻟﺖ ﺍﻟﺸﺮﻳﻌﺔ ﻋﻠﻰ ﻓﻌﻠﻪ ﺣﻴﻨﺌﺬ، ﻛﺠﻤﻊ ﺍﻟﻘﺮﺍﻥ ﻓﻲ ﺍﻟﻤﺼﺤﻒ، ﻭﺟﻤﻊ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻓﻲ ﺍﻟﺘﺮﺍﻭﻳﺢ ﻋﻠﻰ ﺍﻣﺎﻡ ﻭﺍﺣﺪ، ﻭﺗﻌﻠﻢ ﺍﻟﻌﺮﺑﻴﺔ ﻭﺃﺳﻤﺎﺀ ﺍﻟﻨﻘﻠﺔ ﻟﻠﻌﻠﻢ، ﻭﻏﻴﺮ ﺫﻟﻚ ﻣﻤﺎ ﻳﺤﺘﺎﺝ ﺍﻟﻴﻪ ﻓﻲ ﺍﻟﺪﻳﻦ، ﺑﺤﻴﺚ ﻻ ﺗﺘﻢ ﺍﻟﻮﺍﺟﺒﺎﺕ ﺍﻭ ﺍﻟﻤﺴﺘﺤﺒﺎﺕ ﺍﻟﺸﺮﻋﻴﺔ ﺍﻻ ﺑﻪ، ﻭﺍﻧﻤﺎ ﺗﺮﻛﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻟﻔﻮﺍﺕ ﺷﺮﻃﻪ ﺍﻭ ﻭﺟﻮﺩ ﻣﺎﻧﻊ . ﻓﺄﻣﺎ ﻣﺎ ﺗﺮﻛﻪ ﻣﻦ ﺟﻨﺲ ﺍﻟﻌﺒﺎﺩﺍﺕ ﻣﻊ ﺍﻧﻪ ﻟﻮ ﻛﺎﻥ ﻣﺸﺮﻭﻋﺎ ﻟﻔﻌﻠﻪ ﺍﻭ ﺍﺫﻥ ﻓﻴﻪ ﻭﻟﻔﻌﻠﻪ ﺍﻟﺨﻠﻔﺎﺀ ﺑﻌﺪﻩ ﻭﺍﻟﺼﺤﺎﺑﺔ، ﻓﻴﺠﺐ ﺍﻟﻘﻄﻊ ﺑﺎﻥ ﻓﻌﻠﻪ ﺑﺪﻋﺔ ﻭﺿﻼﻟﺔ .(( ﺍﻧﺘﻬﻰ . Ma'ana: ((Dawwamanmen bari Sunnah ce, kamar yadda dawwamanmen aiki yake Sunnah, sabanin abin da barin shi ya kasance ne saboda rashin bukatar yin shi, ko kuwa saboda rashin sharadin yin shi, ko kuwa saboda samuwar abin da ya hana yin shi, sannan bayan (mutuwar Annabi) bukatar yin hakan ta taso, ko sharadin yin hakan ya samu, ko abin da ke hana yin hakan ya kau, ta yadda Shari'ah za ta nuna halaccin yin shi, kamar hada Alkur'ani a Mus'hafi, da hada mutane bayan limami daya a cikin sallar tarawihi, da koyon ilmin Larabci, da haddace sunayen masu nakalto ilmi, da wanin wannan daga cikin abin da ake bukatarsa cikin Addini, ta yadda wajibai da mustahabbai na Shari'ah ba sa cika sai tare da shi, saboda da ma can (Manzon Allah) mai tsira da amincn Allah ya bar yin shi ne saboda kubucewar sharadinsa, ko saboda samuwar abin da ke hana yin shi. To amma abin da (Annabi) ya bari daga jinsin Ibadu tare da cewa da abin wani abu ne da ya dace da Shari'ah to da ya aikata shi, ko da ya ba da izinin a yi shi, kuma da ma Khalifofinsa da Sahabbai sun yi shi a bayansa, (irin wannan kam) wajibi ne a tabbatar da cewa lalle yin shi bidi'ah ce kuma bata)). Intaha. ************************************** Da wannan magana ta Shaikhul Islam Ibnu Taimiyah za mu fahimci cewa: Sunnar Annabi mai tsira da amincin Allah cikin bude taro ko rufe taro da addu'ah ita ce: Barin yin hakan, saboda masu yin haka suna ganin wata ibada suke yi saboda su samu biyan bukatar Duniya da Lahira, wannan shi ya sa ma in sun ga wasu sun yi taro ba tare da sun yi ba sai su rika jin haushinsu, kai, sai ma su rika zaginsu, suna ta yin musu yarfe, da sharri, da jumhuri iri-iri!! ************* MAIDA MARTANI GA MASU BIJIRE WA SUNNAH: Idan wani ya kafa hujja da hadithin Abdullahi Dan Umar wanda Tirmizi ya ruwaito cikin Sunan hadithi na 3,502, da kuma Nasaa'i cikin Sunan hadithi na 10,234 cewa:- (( ﻗﻠﻤﺎ ﻛﺎﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻳﻘﻮﻡ ﻣﻦ ﻣﺠﻠﺲ ﺣﺘﻰ ﻳﺪﻋﻮ ﺑﻬﺆﻻﺀ ﺍﻟﺪﻋﻮﺍﺕ ﻷﺻﺤﺎﺑﻪ : ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺍﻗﺴﻢ ﻟﻨﺎ ﻣﻦ ﺧﺸﻴﺘﻚ ﻣﺎ ﺗﺤﻮﻝ ﺑﻪ ﺑﻴﻨﻨﺎ ﻭﺑﻴﻦ ﻣﻌﺎﺻﻴﻚ، ﻭﻣﻦ ﻃﺎﻋﺘﻚ ﻣﺎ ﺗﺒﻠﻐﻨﺎ ﺑﻪ ﺟﻨﺘﻚ، ﻭﻣﻦ ﺍﻟﻴﻘﻴﻦ ﻣﺎ ﺗﻬﻮﻥ ﺑﻪ ﻣﺼﺎﺋﺐ ﺍﻟﺪﻧﻴﺎ، ﻭﻣﺘﻌﻨﺎ ﺑﺎﺳﻤﺎﻋﻨﺎ ﻭﺍﺑﺼﺎﺭﻧﺎ ﻭﻗﻮﺗﻨﺎ ﻣﺎ ﺍﺣﻴﻴﺘﻨﺎ، ﻭﺍﺟﻌﻠﻪ ﺍﻟﻮﺍﺭﺙ ﻣﻨﺎ، ﻭﺍﺟﻌﻞ ﺛﺎﺭﻧﺎ ﻋﻠﻰ ﻣﻦ ﻇﻠﻤﻨﺎ، ﻭﺍﻧﺼﺮﻧﺎ ﻋﻠﻰ ﻣﻦ ﻋﺎﺩﺍﻧﺎ، ﻭﻻ ﺗﺠﻌﻞ ﻣﺼﻴﺒﺘﻨﺎ ﻓﻲ ﺩﻳﻨﻨﺎ، ﻭﻻ ﺗﺠﻌﻞ ﺍﻟﺪﻧﻴﺎ ﺍﻛﺒﺮ ﻫﻤﻨﺎ ﻭﻻ ﻣﺒﻠﻎ ﻋﻠﻤﻨﺎ، ﻭﻻ ﺗﺴﻠﻂ ﻋﻠﻴﻨﺎ ﻣﻦ ﻻ ﻳﺮﺣﻤﻨﺎ .(( ﺍﻧﺘﻬﻰ . Ma'ana: ((Kadan ne za a ce Mnazon Allah mai tsira da amincin Allah ya tashi daga wata majalisa ba tare da ya yi wa Sahabbansa addu'a da wadannan addu'o'i ba: Ya Allah Ka ba mu wani abu na tsoronKa da zai shiga tsakaninmu da sabonKa, da wani abu na da'arKa da zai kai mu aljannarKa, da wani abu na yakini da zai kai saukaka mana musibun Duniya, ka jiyarda mu dadi da jinmu, da ganinmu, da karfinmu matukar dai Ka rayar da mu, Ka zamar da shi mai gado gare mu, Ka sanya ramuwar gayyarmu a kan wanda ya zalunce mu, Ka taimake mu a kan wanda ya nuna mana kiyayya, kada Ka sanya musibarmu a cikin addininmu, kada Ka sanya Duniya mafi girman hamminmu, ko iya matukar ilminmu, kada Ka dora wanda ba ya tausaya mana a kanmu)). Intaha. Idan wani ya kafa hujja da wannan hadithin to sai a ce da shi: Shi wannan hadithin abin da kawai ya ce shi ne: "Yan lokuta kadan ne za ce Annabi ya tashi daga wata majalisa ba tare da ya yi wa sahabbansa addu'a ba" hadithin bai ce Annabi yana ce wa sahabbansa ne: ku yi salati goma-goma sannan ya rika yin addu'a su kuma suna cewa: ameen ba!!! Babu wani magabaci da ya yi wa hadithin wannan fahimta, babu kuma wani malami daga cikin masu yi wa hadithai sharhi -a iya sanina- da ya yi wa hadithin wannan fahimta, babu daya daga cikin maluman Da'awah da Aqidah da ya yi wa hadithin wannan fahimta!!! Sannan ko shakka babu da da wannan surar ce Annabi yake yin addu'ar to da an nakalto mana ita, saboda sura ce mai jan hankulan mutane sosai, domin kowa ya kan bar abin da yake yi ne domin ya saurari mai yin addu'a bayan ya yi salati sannan kuma ya rika fadar ameen. Sannan a cikin hadithin an ce:- (( ﻣﻦ ﻣﺠﻠﺲ )) Watau: daga ma ko wace majlisa. Ke nan wannan ya hada da majalisar tattauna lamuran duniya na yau da gobe, da majalisar wani darasi, da majalisar koma mene ne. In da kuwa lalle yana yin addu'ar ne a bisa surar da muke yi, to da kuwa an nakalto mana ita. Sannan kuma da Malumanmu na Da'awah da Aqidah ba su hana yin addu'a cikin irin ita wannan surar ba a farko ko karshen majalisar wani darasi, ko majalisar karatun Kur'ani ba, da sauransu. Sannan abu na biyu shi ne: Mene ne ya hada tsakanin cewa Annabi yana yi wa Sahabbansa addu'a cikin mafi yawan majalisu, da kuma cewa Annabi yana addu'ar bude taro da rufe taro cikin jam'i, in ba ta'assubanci da son zuciya ba? Ga misali: Abu Dawuda ya ruwaito hadithi na 3,203, da Tirmizi hadithi na 1,024, da Nasa'ii hadithi na 1,986' da Ibnu Majah hadithi na 1,498, da Ahmad hadithi na 17,581 daga Sahabi Abu Hurairah da waninsa cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya kasance yana yi wa Sahabbai rayayyu da matattu maza da mata manya da yara addu'a cikin sallar janaza. Ga ma yadda nassin yake:- (( ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺍﻏﻔﺮ ﻟﺤﻴﻨﺎ ﻭﻣﻴﺘﻨﺎ ﻭﺻﻐﻴﺮﻧﺎ ﻭﻛﺒﻴﺮﻧﺎ ﻭﺫﻛﺮﻧﺎ ﻭﺍﻧﺜﺎﻧﺎ ﻭﺷﺎﻫﺪﻧﺎ ﻭﻏﺎﺋﺒﻨﺎ . ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻣﻦ ﺍﺣﻴﻴﺘﻪ ﻣﻨﺎ ﻓﺎﺣﻴﻪ ﻋﻠﻰ ﺍﻻﻳﻤﺎﻥ ﻭﻣﻦ ﺗﻮﻓﻴﺘﻪ ﻣﻨﺎ ﻓﺘﻮﻓﻪ ﻋﻠﻰ ﺍﻻﺳﻼﻡ . ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻻ ﺗﺤﺮﻣﻨﺎ ﺍﺟﺮﻩ ﻭﻻ ﺗﻀﻠﻨﺎ ﺑﻌﺪﻩ .(( ﺍﻧﺘﻬﻰ . Ma'ana: ((Ya Allah Ka gafarta wa rayayyunmu da matattunmu, da kanananmu da manyanmu, da mazanmu da matanmu, da halartattunmu da wadanda ba sa nan daga cikinmu. Ya Allah wanda Ka raya shi daga cikinmu to Ka raya shi a kan Imani, Wanda kuma Ka matar daga cikinmu to Ka matar da shi a kan Musulunci. Ya Allah kada Ka haramta mana ladansa, kada kuma Ka batar da mu bayansa)). Intaha. A nan addu'a ce da Annabi yake yi wa Sahabbansa, rayayyu da matattu, amma kuma shi kadai yake yin ta ba ma dole ba ne jama'ar da ke tare da shi su abin da yake fada, kuma babu salatin Annabi goma-goma a cikinta, babu kuma fadar ameen daga sauran jama'a. Lalle yadda ita wannan addu'ar take to haka ma addu'ar:- (( ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺍﻗﺴﻢ ﻟﻨﺎ ﻣﻦ ﺧﺸﻴﺘﻚ ﻣﺎ ﺗﺤﻮﻝ ﺑﻪ ﺑﻴﻨﻨﺎ ﻭﺑﻴﻦ ﻣﻌﺎﺻﻴﻚ ......)). take, wannan shi ya sa ma su wadannan kalmomi ba sa canja wa, kamar yadda wadancan su ma ba sa canjawa. Sannan abu na biyu shi ne: Akwai gurare da yawa da Annabi mai tsira da amincin Allah yake yi wa Sahabbai addu'a, to amma maluman Sunnah ba su fahimci cewa addu'ar jam'i ne yake yi ba. Misali:- 1-Hadithi na 5108 da Abu Dawud ya ruwaito, na 4623 da Abu Ya'ala ya ruwaito cikin Musnad, na 140 da Ibnul Jaaruud ya ruwaiton cikin Muntaqa daga A'isha Allah Ya kara mata yarda ta ce:- (( ﻛﺎﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻳﺆﺗﻰ ﺑﺎﻟﺼﺒﻴﺎﻥ ﻓﻴﺪﻋﻮ ﻟﻬﻢ ﺑﺎﻟﺒﺮﻛﺔ .(( ﺍﻧﺘﻬﻰ . Ma'ana: ((Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya kasance ana zuwa masa da yara yana musu addu'ar samun albarka)). Intaha. Wannan hadithin Albanii ya inganta shi cikin Alkalimut Tayyib 1/162. Lalle a nan hadthin ba ya nufin jam'in addu'a Annabi yake yi watau ya umurci mutane su daga hannu suna cewa Ameen shi kuwa yana Ddu'a. 2-Hadithi na 502 da Bukharii ya ruwaito cikin Al'adabul Mufrad, da hadithi na 9969 da Baihaqii ya ruwaito cikin Shu'abul Iman cewa:- (( ﺟﺎﺀﺕ ﺍﻟﺤﻤﻰ ﺍﻟﻰ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻓﻘﺎﻟﺖ : ﺍﺑﻌﺜﻨﻲ ﺍﻟﻰ ﺍﺛﺮ ﺍﻫﻠﻚ ﻋﻨﺪﻙ . ﻓﺒﻌﺜﻬﺎ ﺍﻟﻰ ﺍﻷﻧﺼﺎﺭ ﻓﺒﻘﻴﺖ ﻋﻠﻴﻬﻢ ﺳﺘﺔ ﺍﻳﺎﻡ ﻭﻟﻴﺎﻟﻴﻬﻦ ﻓﺎﺷﺘﺪ ﺫﻟﻚ ﻋﻠﻴﻬﻢ ﻓﺎﺗﺎﻫﻢ ﻓﻲ ﺩﻳﺎﺭﻫﻢ ﻓﺸﻜﻮﺍ ﺫﻟﻚ ﺍﻟﻴﻪ، ﻓﺠﻌﻞ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻳﺪﺧﻞ ﺩﺍﺭﺍ ﺩﺍﺭﺍ ﻭﺑﻴﺘﺎ ﺑﻴﺘﺎ ﻳﺪﻋﻮ ﻟﻬﻢ ﺑﺎﻟﻌﺎﻓﻴﺔ .(( ﺍﻧﺘﻬﻰ . Ma'ana: ((Zazzabi ya zo gurin Annabi mai tsira da amincin Allah sai ya ce: aika ni zuwa ga mutanen da suka fi soyuwa gare ka. Sai ya aika da shi zuwa ga Ansarawa, ya je ya zauna a cikinsu yini shida da dare shida, hakan ya tsananta a kansu, sai ya je musu cikin unguwarsu, sai suka yi masa kukan wannan zazzabin. Sai Annabi mai tsira da amincin Allah ya rika shiga bangare bangare, gida gida yana musu addu'ar samun lafiya)). Intaha. Wannan hadithin Albaanii ya inganta shi cikin Silsilah Sahihah lamba na: 2502. A nan ma babu wani mai sharhin hadithai da ya ce addu'ar jam'i aka yi Annabi na addu'a saura jama'a na cewa: ameen. 3-Hadithi na 1668 da Malik ya ruwaito cikin Muwattaa, da hadithi na 17,959 da Tabaraanii ya ruwaito cikin Almu'ujamul Kabir, da hadithi na 9,503 da Abdur Razzaq ya ruwaito cikin Musannaf daga Abu Burdah cewa:- (( ﺍﻥ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻳﻮﻡ ﺣﻨﻴﻦ ﺃﺗﻰ ﺍﻟﻘﺒﺎﺋﻞ ﻳﺪﻋﻮ ﻟﻬﻢ .(( ﺍﻧﺘﻬﻰ . Ma'ana: ((Annabi mai tsira da amincin Allah ya je wa Kabilu a ranar yakin Hunain yana musu addu'a)). Intaha. Mai littafin Majma'uz Zawaa'id 5/407 ya ce: Mazajen isnadin Mazajen Buharii da Muslim ne, in banda Abdullahi Ibnul Mugiirah shi kuwa thiqah ne. A nan ma babu wanda ya ce Annabi ya je yana addu'ar ne sannan ya umurci Kabilun da su rika cewa: ameen. 4- Hadithi na 4,546 da Haakim ya ruwaito cikin Mustadrak daga Waliid Dan Uqbah cewa:- (( ﻟﻤﺎ ﻓﺘﺢ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻣﻜﺔ ﺟﻌﻞ ﺍﻫﻞ ﻣﻜﺔ ﻳﺄﺗﻮﻥ ﺑﺼﺒﻴﺎﻧﻬﻢ ﻓﻴﻤﺴﺢ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻋﻠﻰ ﺭﺅﻭﺳﻬﻢ ﻭﻳﺪﻋﻮ ﻟﻬﻢ .(( ﺍﻧﺘﻬﻰ . Ma'ana: ((Lokacin da Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya bude Makka, mutanen Makka sun yi ta kawo yaransu Manzon Allah yana ta shafan kawunansu yana musu addu'a)). Intaha. A nan ma babu wani mai sharhin hadithi da ya ce: Annabi ya ce su yi ta cewa ameen ne a lokacin da yake yi wa yaran nasu addu'a. watau babu wanda ya ce addu'ar jam'i Annabi ya yi. **************************************** AMSA A KAN WATA MAGANAR KUMA: Idan wani ya kafa hujja da wadannan Nassosi kamar:- (( ﻭﺍﻟﺬﻳﻦ ﺟﺎﺀﻭﺍ ﻣﻦ ﺑﻌﺪﻫﻢ ﻳﻘﻮﻟﻮﻥ ﺭﺑﻨﺎ ﺃﻏﻔﺮﻟﻨﺎ ﻭﻻﺧﻮﺍﻧﻨﺎ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺳﺒﻘﻮﻧﺎ ﺑﺎﻹﻳﻤﺎﻥ .(( ﺍﻟﺤﺸﺮ :١٠ . Ma'ana: ((Wadanda suka zo daga bayansu suna cewa: Ya Ubangijinmu! Ka gafarta mana, da kuma 'yan'uwanmu wadanda suka riga mu yin Imani)). Intaha. Da kuma:- (( ﻗﻞ ﻣﺎ ﻳﻌﺒﺆ ﺑﻜﻢ ﺭﺑﻲ ﻟﻮﻻ ﺩﻋﺎﺅﻛﻢ .(( ﺍﻟﻔﺮﻗﺎﻥ : ٧٧ . Ma'ana: ((Ka ce: Ubangijina ba ya kulawa da ku, in ba domin addu'arku ba)). Intaha. Da kuma:- (( ﻭﺍﺫﺍ ﺳﺎﻟﻚ ﻋﺒﺎﺩﻱ ﻋﻨﻲ ﻓﺎﻧﻲ ﻗﺮﻳﺐ ﺃﺟﻴﺐ ﺩﻋﻮﺓ ﺍﻟﺪﺍﻉ ﺍﺫﺍ ﺩﻋﺎﻥ .(( ﺍﻟﺒﻘﺮﺓ : ١٨٦ . Ma'ana: ((Idan bayiNa suka tambaye ka labariNa to Ni kusa Nake, kuma ina amsa addu'ar mai addu'a in ya kira Ni)). Intaha. Da kuma sauran Nassosi masu kama da haka ya ce kuma: Lalle mu muna hana a yi sa Musulmi addu'a ne, alhalin Allah Ya ce a roke Shi zai kuma amsa!!! Farko dai sai a ce da su tarihi ne yake maimaita kan sa, tsakanin maluman Sunnah da kuma masu bidi'a da bautar son zuciya. Misali: lokacin da Shehu Uthmanu Dan Fodiyo ya ce cikin littafin shi Ihya'us Sunnah shafi na 102:- (( ﻭﻣﻦ ﺫﻟﻚ ﺍﻟﺪﻋﺎﺀ ﺩﺑﺮ ﺍﻟﺼﻼﺓ ﺑﻜﻴﻔﻴﺔ ﻣﻌﻠﻮﻣﺔ ﻭﻫﻮ ﺍﻥ ﻳﺪﻋﻮ ﺍﻻﻣﺎﻡ ﻭﻳﺆﻣﻦ ﺍﻟﻨﺎﺱ، ﻭﻫﻮ ﺑﺪﻋﺔ ﻣﻜﺮﻭﻫﺔ ﻓﻲ ﻣﺬﻫﺐ ﻣﺎﻟﻚ .(( ﺍﻧﺘﻬﻰ . Ma'ana: ((Daga cikin wannan akwai addu'a bayan Salla a bisa wani yanayi sananne, shi ne kuwa: Liman yana addu'a Mamu suna cewa ameen. Shi wannan bidi'a ce makruuhiya a cikin mazhabar Imam Malik)). Intaha. A lokacin da Shehu Dan Fodiyo da kuma ire-irensa suka fadi haka saboda neman jama'a su yi Musuluncisu kamar yadda Annabi da Sahabbai suka yi an samu wasu masu ta'assubanci wadanda kiyayya da hasada suka cika zukatansu, da suka ki yin aiki da wannan bayani na ilmi da so wa Musulmi alheri, suka koma suna ta kafa hujja da irin wadannan dalilai aammah, wadanda masu ilmi sun san cewa ba za nuni a kan bigiren da aka yi sabani a kan shi. Kamar dai mutumin da za ka ce da shi: ka daina yin Salatul fatih ka rika yin Salatin da Annabi mai tsira da amincin Allah ya koya wa Sahabbai. Sannan shi kuma ya rika gaya wa jama'a cewa: Kai din nan ka hana a rika yi wa Annabi salati!!! Ko kuma ka ce a daina zikirin bidi'ah na ihu da bugun kirji, ko bisa wani adadi wanda ba Shari'a ce ta bayyana ba. Sai kuma a ce: Kai din nan wai ka hana a yi wa Allah zikiri duk kuwa da cewa Nasosi da yawa sun yi umurni da yin hakan!! Na biyu sai a ce da su: Irin wannan tuhumar ba sabon lamari ba ne ga Maluma masu da'awah wadanda suke kokarin maida mutane a kan Sunnar Annabi mai tsira da amincin Allah cikin dukkan lamuransu. Imam Abdur Razzaq ya ruwaito cikin littafinsa Musannaf atharii na 4,755 da kuma Imamul Baihaqii a cikin Assunanul Kubra atharii na 4,621 daga Sa'id Dan Musayyib cewa:- (( ﺍﻧﻪ ﺭﺃﻯ ﺭﺟﻼ ﻳﺼﻠﻲ ﺑﻌﺪ ﻃﻠﻮﻉ ﺍﻟﻔﺠﺮ ﺍﻛﺜﺮ ﻣﻦ ﺭﻛﻌﺘﻴﻦ ﻳﻜﺜﺮ ﻓﻴﻬﺎ ﺍﻟﺮﻛﻮﻉ ﻭﺍﻟﺴﺠﻮﺩ، ﻓﻨﻬﺎﻩ، ﻓﻘﺎﻝ : ﻳﺎ ﻣﺤﻤﺪ ! ﻳﻌﺬﺑﻨﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺼﻼﺓ؟ ﻗﺎﻝ : ﻻ ﻭﻟﻜﻦ ﻳﻌﺬﺑﻚ ﻋﻠﻰ ﺧﻼﻑ ﺍﻟﺴﻨﺔ .(( ﺍﻧﺘﻬﻰ . Ma'ana: ((Ya ga wani mutum yana salla fiye da raka'a biyu bayan fitowar alfijir yana yawaita ruku'i da sujjada cikin sallar, sai ya hana shi. Sai mutumin ya ce: Ya Abu Muhammad! Yanzu a kan salla ne Allah zai azabtar da ni? Sai ya ce: A'a zai azabtar da kai ne a kan sabawa Sunnah)). Intaha. Sheik Albani bayan ya kawo wannan magana cikin littafinsa Irwa'ul Galil 2/236 kuma ya inganta isnadinta sai ya ce:- (( ﻭﻫﺬﺍ ﻣﻦ ﺑﺪﺍﺋﻊ ﺃﺟﻮﺑﺔ ﺳﻌﻴﺪ ﺑﻦ ﺍﻟﻤﺴﻴﺐ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ، ﻭﻫﻮ ﺳﻼﺡ ﻗﻮﻱ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻤﺒﺘﺪﻋﺔ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻳﺴﺘﺤﺴﻨﻮﻥ ﻛﺜﻴﺮﺍ ﻣﻦ ﺍﻟﺒﺪﻉ ﺑﺎﺳﻢ ﺍﻧﻬﺎ ﺫﻛﺮ ﻭﺻﻼﺓ، ﺛﻢ ﻳﻨﻜﺮﻭﻥ ﻋﻠﻰ ﺍﻫﻞ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﺍﻧﻜﺎﺭ ﺫﻟﻚ ﻋﻠﻴﻬﻢ، ﻭﻳﺘﻬﻤﻮﻧﻬﻢ ﺑﺎﻧﻬﻢ ﻳﻨﻜﺮﻭﻥ ﺍﻟﺬﻛﺮ ﻭﺍﻟﺼﻼﺓ !! ﻭﻫﻢ ﻓﻲ ﺍﻟﺤﻘﻴﻘﺔ ﺍﻧﻤﺎ ﻳﻨﻜﺮﻭﻥ ﺧﻼﻓﻬﻢ ﻟﻠﺴﻨﺔ ﻓﻲ ﺍﻟﺬﻛﺮ ﻭﺍﻟﺼﻼﺓ ﻭﻧﺤﻮ ﺫﻟﻚ .(( ﺍﻧﺘﻬﻰ . Ma'ana: ((Wannan yana daga cikin kyawawan jawaban Sa'idu Dan Musayyib Allah Madaukakin Sarki Ya yi masa rahama, sannan kuma shi makami ne mai karfi a kan 'yan bidi'a da suke ganin kyawun da yawa daga cikin bidi'o'i da sunan cewa: Ai zikiri ne, da Salla! Sannan kuma su yi wa Ahlus Sunnah inkarin inkarin da suke yi musu, kuma su tuhumce su da cewa: Suna hana zikirin Allah da kuma Salla!! Wanda kuma a gaskiyar al'amari su suna musu inkarin barin Sunnah ne da suka yi cikin Zikirin da kuma Sallar, da abin da ya yi kama da haka)). Intaha. Muna rokon Allah Madaukakin Sarki ya nuna mana gaskiya gaskiya ce ya kuma ba mu ikon aiki da ita. Ya kuma nuna mana karya karya ce ya ba mu ikon guje mata. Ameen.
Back to posts
This post has no comments - be the first one!

UNDER MAINTENANCE

XtGem Forum catalog